in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da rahoto game da yanayin hakkin dan adam a Amurka
2019-03-14 15:17:13 cri
A yau Alhamis kasar Sin ta wallafa wani rahoto game da yanayin hakkin dan adam a kasar Amurka.

Rahoton, mai taken "Bayanan hakkin dan adam na Amurka a shekarar 2018," wanda ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar, ya zama wani takwaran rahoto ga rahotanni game da yanayin kare hakkin bil adama na shekarar 2018, wanda ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a ranar 13 ga watan Maris, agogon wurin.

Rahoton na kasar Sin ya ce, gwamnatin Amurka, tana aiwatar da wani salo ne na kashin kanta game da batun kare hakkin dan adam, akwai batutuwan da aka tattara game da keta hakkin dan adam wadanda ke kunshe da kura kurai masu yawa cikinsa da kuma rashin hikima cikinsa, sai dai kasar Amurka ta kan raba kafa dangane da ra'ayinta na kare hakkin dan Adam, in ji rahoton da kasar Sin ta gabatar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China