Rahoton ya ce, a 2019, ma'aikatar za ta yi kokarin ganin kaso 98 na kauyuka sun samu tsarin sadarwa na 4G, sannan kaso 98 na kauyuka masu fama da talauci sun samu tsarin sadarwa na intanet.
Ya kara da cewa, a bana, farashin matsakaicin tsarin sadarwa zai ragu da kaso 15 ga kanana da matsakaitan kamfanoni, yayin da matsakaicin tsarin sadarwar intanet na tafi da gidanka zai ragu da akalla kaso 20.
Ma'aikatar ta kuma lashi takobin gaggauta amfani da fasahar 5G a bangaren kasuwanci da kuma magance matsaloli da suka hada da yawan kiran waya ba bisa ka'ida da kuma yawan cire kudin hidima.( Fa'iza Msutapha)