in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD ta amince Sin ta halarci taron rahoton binciken yanayin hakkin dan Adam zagaye na uku
2019-03-16 17:11:42 cri

Majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD ta amince da Sin ta halarci taron tantance hakkin dan Adam na kasashen duniya zagaye na uku.

Shugaban tawagar wakilan kasar Sin kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Le Yucheng ya bayyanawa 'yan jarida bayan taron cewa, majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD ta amince Sin ta halarci taron binciken yanayin 'yancin hakkin dan Adam da kasashen duniya ke ciki. Le Yucheng ya kuma yi bayani game da taron, inda ya ce, an amince da yanayin hakkin dan Adam na Sin, da hanya da ta dace da kasar Sin ke bi, da kuma imanin kasar Sin kan aikin kiyaye hakkin dan Adam.

A yayin taron, wakilan kasashen Nijeriya, da Mali, da Mauritania, da Namibia, da Pakistan, da Philippines da sauransu, sun yaba da nasarorin da Sin ta samu wajen kare hakkin dan Adam , kokarin da kasar Sin ta yi bayan saurari shawarwarin da kasa da kasa suka ba ta. Haka kuma sun nuna goyon baya ga kudurin majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD.

Le Yucheng ya mayar da martani ga zargin da wasu wakilan kasashen yammacin duniya da hukumomin da ba na gwamnati ba suka yiwa kasar Sin ba tare da hujja ba, yana mai cewa, Sin ba za ta amince da duk wane nau'i na tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida, da kawo illa ga 'yancin mallakar kasar da cikakken yankinta ta hanyar yin amfani da hujjar kare hakkin dan Adam ba. Kana ya jaddada cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan raya sha'anin 'yancin dan Adam ta hanyarta ta halayyar musamman mai dacewa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China