Wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, ta ce Antonio Guterres ya yi jimamin aukuwar mummunan lamarin da ya haifar da asarar rayuka.
Sakatare Janar din Ya kuma jajanta tare da mika ta'aziyyarsa ga iyalai da makusantan wadanda lamarin ya rutsa da su, ciki har da na jami'an MDD da kuma gwamnati da al'ummar Habasha.
Sanarwar ta kara da cewa, MDD na tuntubar hukumomin Habasha, kuma suna aiki tare domin samar da bayanan jami'an majalisar da hatsarin jirgin ya rutsa da su.
Da safiyar jiya Lahadi ne dukkan mutane 157 dake cikin jirgin saman Ethiopian suka mutu sanadiyyar hatsarin da jirgin ya yi.
Jirgin samfurin Boeing 737-800MAX, da ya nufi Nairobin Kenya, ya tashi ne da misalin karfe 8:38 na safe agogon Habasha, daga birnin Addis Ababa, da misalin karfe 08:44 ne kuma aka kasa tuntubarsa. (Fa'iza Mustapha)