Yu Jianhua, shi ne jagoran tawagar ta Sin, a taron na MDD dake gudana a birnin Geneva. Yayin wani taro da ya gudana a gefen babban taron, ya bayyana cewa, yankin Xinjiang a yanzu, na samun ci gaba cikin sauri, da daidaito sama da wanda ya taba samu a baya. Kaza lika daukacin kabilun yankin na samun kariyar da ta dace ta fuskar tattalin arziki, da siyasa, da zamantakewar al'umma, da raya al'adu, da kuma kare hakkin muhalli.
Sai dai a cewar Yu Jianhua, saboda dalilai na siyasa, wasu na yada jita jita, da karairayi, game da abun da ke faruwa a yankin na Xinjiang, da nufin bata sunan Sin da gwamnatin ta. Sai dai kuma jami'in ya ce ko shakka babu, masu wannan ra'ayi ba za su yi nasara ba, duba da irin nasarori, da ci gaba, da daidaito, da hadin kai da ake samu a yankin na Xinjiang.
Jami'in ya kara da cewa, samar da ilimin sana'o'i, da cibiyar horaswa dake Xinjiang sun dace da bukatar yankin. Har ila yau kasar Sin ba za ta taba barin 'yan ta'adda, da masu tsattsauran ra'ayin addini, su tarwatsa abubuwa muhimmai da al'ummar yankin Xinjiang suka gina domin samar da ingantacciyar rayuwa ba.(Saminu Alhassan)