in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a gaggauta daukar matakai kan matsalar sauyin yanayi
2019-03-14 10:17:59 cri

MDD ta yi kira a gaggauta daukar matakai kan matsalar sauyin yanayi don ganin an cimma nasarar manufofin samun ci gaba mai dorewa (SDGs).

Wannan kira na kunshe ne cikin rahoto na shida game da yanayin muhalli na duniya (GEO-6), inda ya bukaci gaggauta daukar matakai, domin duk wani jinkiri yana kara yawan kudaden da za a kashe wajen cimma manufofin muradun na SDGs da yarjejeniyar matakan sauyin yanayi ta birnin Paris.

Rahoton wanda aka kaddamar jiya Laraba a gefen taro na 4 na MDD kan sauyin yanayi dake gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, ya bayyana cewa, a halin yanzu duniya ba ta kama hanyar cimma nasarar manufofin samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2020 ko 2050 ba.

Rahoton ya kuma nuna cewa, idan har kasashe suka zuba jarin kaso 2 cikin 100 na GDPn su a fannin kare muhalli, hakan zai taimaka wajen samun ci gaba na dogon lokaci, fiye da yadda aka yi hasashe yanzu, amma ba zai yi wani babban tasiri a bangaren sauyin yanayi, karancin ruwa da yanayin muhallin halittu ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China