Wasu rahotannin da aka wallafa sun nuna cewa an kashe wani jami'in dan sanda guda, kana an harbi wani ma'aikacin lafiya, sai dai ana sa ran zai iya farfadowa, harin dai an kaddamar da shi ne a ranar Asabar a gabashin birnin Butembo dake DRC.
Kakakin MDD ya fadawa manema labarai cewa shugaban hukumar lafiya ta duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ziyarci cibiyar bayan harin da aka kaddamar a ranar Asabar. An kuma kaddamar da wani harin a makon da ya gabata, in ji hukumar ta WHO.
Ziyarar na zuwa ne yayin da babban jami'in lafiya na MDDr ke kammala ziyararsa ta aiki na kwanaki uku a kasar, inda ya gana da wasu jami'an gwamnatin kasar, da kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu na ciki da wajen kasar.
Ya bayyana fargaba game da hasarar rai da kuma jikkatar mutane da aka samu a sandiyyar hare-haren. Ya ce ba su da wani zabi da ya rage illa ci gaba da ceto rayukan jama'a a wannan waje, inda ya bayyana wajen a matsayin daya daga cikin wurare mafiya hadari a duniya. (Ahmad Fagam)