Firaministan ya ce, kasar Sin na bin wani tsari kan jarin waje, wato masu zuba jari na kasashen ketare za su samu dama iri daya da takwarorinsu na kasar Sin, a yayin da suke neman zuba jari a kasuwar kasar, baya ga haka, ban da sassan da baki 'yan kasuwa da a baya ba za su iya zuba jari ba, baki 'yan kasuwa za su samu matsayin daya da takwarorinsu na kasar Sin wajen zuba jari a kasar. A bana kuma za a kaddamar da sabbin sassan da baki ba za su zuba jari ba. Baya ga haka, kasar za ta gyara dokar 'yancin mallakar fasaha, za kuma ta kafa tsarin yanke hukunci kan wadanda suka karya dokar 'yancin mallakar fasaha.
Firaministan ya kuma nuna cewa, an zartas da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa a zaman taro na 2, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13. Game da hakan, ya jaddada cewa, gwamnatin kasar za ta kaddamar da jerin dokoki, da takardu bisa wannan doka, don kiyaye iko da moriyar baki 'yan kasuwa. (Bilkisu)