Kamfanin ya shirya zuba jarin yuan biliyan 4.6, kwatankwacin dala miliyan 676 domin gudanar da aikin a wannan shekarar, ana sa ran aikin zai amfanawa magidanta 316,000 a yankunan Hotan, Kashgar, Kizilsu dake kudancin jahar Xinjiang.
An tsara aikin ne domin maye gurbin makamashin kwal da ake amfani da shi a matsayin babbar hanyar samar da lantarki a yankunan, matakin zai taimakawa mazauna karkara a yankunan wajen samun makamashin samar da dumi a farashi mai sauki kana zai taimaka wajen ba da kariya da kyautata muhallin yankunan.
Yankunan suna karshen yankin hamadar Taklimakan ne, kuma shine hamada mafi girma a kasar Sin, kana itace hamada ta biyu mafi girma a duk fadin duniya, inda yanayin wajen ke haifar da tsananin talauci ga mazauna wuraren.