in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta halarci taron binciken rahoton hakkin dan Adam na Sin zagaye na uku na majalisar hakkin dan Adam ta MDD
2019-03-13 20:32:54 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Laraba cewa, Sin za ta halarci taron binciken rahoton hakkin dan Adam na Sin zagaye na uku na majalisar hakkin dan Adam ta MDD a ranar 15 ga wannan wata.

Lu Kang ya bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci kan aikin binciken rahoton hakkin dan Adam, za kuma ta tura tawagarta wadda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng zai jagoranta, wadda za ta kunshi wakilan hukumomin gwamnatin kasar da na yankunan Xinjiang, da Tibet, da Hong Kong, da Macau don halartar taron. Sin za ta yi bayani game da bin shawarwarin da kasa da kasa suka gabatar a gun taron binciken rahoton a watan Nuwanba na bara, tare da yin mu'amala da bangarori daban daban da abun ya shafa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China