in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara zuba jari a masana'antu masu tasowa
2019-03-14 10:31:18 cri
Wasu bayanan da jaridar Daily ta kasar Sin ta fitar game da tattalin arziki a jiya Laraba ya nuna cewa hukumar sauye sauye da raya cigaban kasar Sin ta ce masana'antun dake tasowa na kasar Sin za su samu karuwar zuba jari a cikin wannan shekarar.

Kasar Sin za ta kara tallafawa wasu shirye shirye da zuba jari a fannin kayayyakin more rayuwa a kamfanoni masu tasowa a shekarar 2019, wanda ya kunshi tsarin fasahar sadarwa ta zamani ta 5G, da na'urori masu amfani da fasaha da kansu (AI), da kamfanonin intanet da kayayyakin intanet, kamar yadda hukumar raya cigaba da yin gyare gyare ta kasar wato (NDRC) ta sanar.

Gwamnatin Sin za ta samar da wani yanayin duba tsarin kamfanoni masu tasowa da irin tasirinsu ga kasuwanni da kuma irin alfanun da za su haifar wajen kawo sauye sauye ta fuskar raya cigaban tattalin arziki, kamar yadda kamfanin jaridar ya bada rahoton cikin kalaman da Ren Zhiwu, wato mataimakin babban sakataren hukumar NDRC, ya bayyana.

Kananan hukumomi su ma zasu dauki matakan tallafawa kamfanoni masu tasowa don ba su tallafin kudade, da fasahar kirkire kirkire, da samar da yanayin kasuwanci mai inganci. Za'a cigaba da yin kokari don bunkasa kwarewar kamfanonin masu tasowa, in ji rahoton jaridar. (Ahamad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China