in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kafa sabuwar gwamnati a Sudan
2019-03-14 09:59:24 cri

A jiya ne shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, ya ba da wata doka ta kafa sabuwar gwamnati mai ministoci 19. Firaministan kasar Mohamed Tahir Ella, shi ne ya sanar da dokar yayin wani taron manema labarai a Khartuom, babban birnin kasar.

A bisa tsarin dokar, an nada Fadul Abdalla Fadul a matsayin minista a fadar shugaban kasa, sai kuma Ahmed Sa'ad Omer wanda ya zama minista a majalisar ministocin kasar.

Sauran sun hada da Barakat Musa Al-Hawati wadda aka nada a matsayin ministar hukumar harkokin gwamnatin tarayyar, Bushara Gumaa Aro ministan harkokin cikin gida, Al-Dirdiri Mohamed Ahmed shi ne ministan harkokin kasashen waje, sai Mohamed Ahmed Salem kuma ministan tsaro.

Magdi Hassan Yassin shi aka nada a matsayin ministan kudi, yayin da Al-Khair Al-Nur Al-Mubarak ya zama ministan ilimi. Haka kuma an nada ministocin kwadago, da cinikayya da aikin gona da yawon shakatawa da kuma lafiya.

A ranar 22 ga watan Fabrairu ne dai, shugaba Al-Bashir ya ayyana dokar-ta-baci a fadin kasar, ya kuma rushe gwamnatin tsakiya da jihohin kasar, sakamakon boren gama garin da 'yan kasar suka fara tun ranar 19 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, saboda tabarbarewar tattalin arziki da tsadar farashin muhimamman kayayyakin masarufi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China