in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sudan da Habasha za su rattaba hannu kan yarjejeniyar tura dakaru iyakokinsu
2019-03-13 09:42:11 cri
Kasashen Sudan da Habasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya, jiya Talata a birnin Khartoum, da nufin tura jami'an tsaro na hadin gwiwa zuwa iyakar da ta raba kasashensu.

Taron da aka yi tsakanin kwamitin sojin Sudan da na Habasha, da ya gudana a Khartoum babban birnin Sudan tsakanin ranar 10 zuwa 12 ga wata, ya yi nazarin batutuwan dake da alaka da hadin gwiwa a fannin ayyukan soji da kuma hanyoyin inganta su.

Taron ya kuma tattauna kan farfado da matakan dake da alaka da tsaron iyaka da yaki da masu fasa kauri da laifukan da ake aikatawa tsakanin iyakoki da matakan wanzar da zaman lafiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China