Wakilin kasar Sin ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya sake bitar takunkuman da ya sanya wa kasar Sudan bisa yanayin da kasar take ciki a halin yanzu, sannan daga bisani ya dage takunkuman.
Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kan kasashen Sudan da Sudan ta Kudu jiya Litinin 25 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce yanayin tsaro a yankin Darfur na kasar Sudan ya daidaita, bayan rundunar shirin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar Tarayyar Afirka wato AU dake aiki a yankin wato UNAMID, ta mika ragamar tsaron yankin ga jami'an tsaron gwamnatin kasar a bara.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta yaba da gudunmuwar rundunar UNAMID wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na Darfur, sannan tana maraba da gwamnatin kasar Sudan ta yi kokarin inganta tsarin shugabanci da na tsaro.
Ya ci gaba da cewa, a daya bangaren kuma, har yanzu Darfur na fuskantar kalubalen da suka hada da rikicin kabilanci da 'yan gudun hijira da ci gaban zaman takewa da tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)