in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da yarjejeniyar Sudan ta kudu tare da kyawawan sauye sauye
2019-03-09 17:34:30 cri

Yarjejeniyar zaman lafiya ta Sudan ta kudu na ci gaba da gudana watanni 6 bayan rattaba mata hannu, inda ake ganin kyawawan sauye sauye.

David Shearer, manzon musamman na Sakatare Janar na MDD a Sudan ta Kudu, ya shaidawa kwamitin sulhu na majalisar cewa, yarjejeniyar alama ce ta kokarin bangarorin da suka aminta da juna kuma suka kuduri niyyar aiki tare domin samun zaman lafiya mai dorewa.

A watan Satumban 2018 ne, gwamnatin Sudan ta Kudu da bangarori masu dauke da makamai suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a kasar Habasha, bayan shafe shekaru 5 ana gwabza fada.

Sudan ta kudu wadda ta samu 'yancin kai daga Sudan a shekarar 2011, ta fada cikin rikicin kabilanci ne a watan Disamban 2013, a lokacin da dakarun dake biyayya ga shugaba Salva Kiir suka fara fada da takwarorinsu dake goyon bayan Riek Machar, tsohon mataimakin shugaban kasar.

Matakin tsarin zaman lafiya da ake ciki a yanzu kafin lokacin sauya gwamnati, zai kare ne a ranar 12 ga watan Mayu. Bisa yarjejeniyar, ana sa ran sabuwar gwamnatin da mataimakan shugaban kasa, ciki har da Riek Machar su fara aiki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China