Darajar hannayen jarin kamfanin Boeing take matsayin koli tun a ranar Laraba, inda ya karu da kashi 1.6 bisa 100, amma ya samu koma baya ne jim kadan bayan da Amurka da Canada suka bada sanarwar daina amfani da jirgin saman na 737 Max.
Amurka za ta daina amfani da dukkan samfurin jirgin na Boeing 737 Max 8 da 9, in ji shugaban kasar Amurkar Donald Trump, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin da Amurka ta kasance babbar kasa ta karshe data dauki wannan mataki bayan da aka samu hadarin samfurin jirgin saman sau biyu a cikin wasu watanni.
Kasashen biyu sun bi sahun sauran kasashen duniya, da suka hada da kasar Sin, kasashen tarayyar turai, da Indonesia, na daina amfani da dukkan samfurin jirgin saman bayan mummunan hadarin da jirgin yayi sau biyu a jere a cikin watanni biyar, ciki har da hadarin ranar Lahadin da ta gabata. (Bello Wang)