in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Trump ya amince da barin sojojin Amurka a Syria
2019-03-06 11:04:09 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya mayar da martani ga 'yan majalisar dokokin kasarsa cewa, ya amince da barin dakarun kasar a kasar Syria.

A ranar 22 ga watan Fabreru ne wani ayarin 'yan majalisun wakilai da dattijai daga jam'iyyu 2 na kasar suka rubuta wasika ga shugaba Trump, inda suka yabawa matakinsa na barin wani adadin sojojin kasar a Syria, a matsayin dakarun wanzar da zaman lafiya.

Kwafin wasikar da kafar yada labarai ta NBC ta samu, ya nuna wani sashe da shugaba Trump ya jaddada manufofin Amurka na ci gaba da kasancewarta a Syria.

A ranar 21 ga watan Fabreru ne Fadar White House ta sanar da cewa, Amurka za ta bar kimanin dakaru 200 a Syria bayan shirinta na ficewa daga kasar. Trump ya tabbatar a kashegari cewa za a bar wani adadi kalilan na dakarun Amurka da za su kasance tare da dakarun wasu kasashe. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China