Pompeo ya gana da manzon musamman mai kula da batun Syria na babban sakataren MDD Geir Pedersen a ranar 5 ga wata a birnin Washington, inda suka tattauna shirin warware batun Syriar. Pompeo ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Amurka ta nuna goyon baya ga MDD da ta yi kokarin warware rikicin Syria ta hanyar matakan siyasa, wadanda suka hada da ayyukan yin kwaskwarima kan kundin tsarin mulkin kasar Syria, da yin shirye-shirye don gudanar da zaben shugaban kasar cikin 'yanci da adalci da sauransu. (Zainab)