in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa sun gama ganawa kafin lokacin da aka tsara
2019-03-01 11:17:15 cri

An kammala ganawa karo na 2 tsakanin shugabannin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa jiya da yamma, kafin lokacin da aka tsara, a birnin Hanoi na kasar Vietnam. Shugabannin ba su daddale wata yarjejeniya ba, saboda sabanin da ke tsakaninsu kan soke takunkumin da aka sanya wa Koriya ta Arewa da kuma matakan kawar da nukiliya daga Koriya ta Arewa.

Yayin taron manema labaru da aka yi bayan ganawar, shugaba Donald Trump na Amurka ya ce, ganawar ta yini 2 da aka yi tsakaninsa da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un ta samu ci gaba, amma ba su daddale wata yarjejeniya ba. Kana sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce, kasashen 2 sun samu ci gaba a yayin ganawar, amma Koriya ta Arewa ba ta biya karin bukatun Amurka ba. Ya ce duk da haka, kasashen 2 suna sa ran sake ganawa tsakanin tawagoginsu nan gaba ba dadewa ba.

A safiyar yau Jumma'a a Hanoi ne, ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa Ri Yong-ho ya ce, yayin ganawar, kasarsa ta bukaci Amurka ta soke wasu takunkumai, inda a nata bangare za ta rufe ginin sarrafa sinadarin nukiliya na Yongbyon har abada. Kuma da ma kasarsa ta shirya rubuta alkawarinta na daina gwaje-gwajen nukiliya da roka mai cin dogon zango har abada, a kokarin rage damuwar Amurka. Amma sai Amurka ta bukaci kasarsa ta kara daukar wani mataki, ban da rufe ginin da ke Yongbyon, wanda hakan ya nuna cewa, Amurka ba ta shirya karbar shawarar Koriya ta Arewa ba tukuna. Ri Yong-ho ya jaddada cewa, in Amurka tana son farfado da tattaunawar, Koriya ta Arewa ba za ta sauya matsayinta ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China