in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Iran: Kasarsa ba za ta yi shawarwari tare da Amurka ba
2019-03-07 13:47:55 cri

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ba da jawabi ta gidan talabijin a jiya Labara, inda ya bayyana cewar, tattalin arzikin kasar Iran ya samu matsi sosai sakamakon takunkumin da Amurka ta sanya mata, amma Iran ba za ta yi shawarari tare da Amurka ba. Ainihin dalilin da ya sa Amurka ta yi hakan shi ne hambarar da mulkin Iran na yanzu, a maimakon batu ne da ya shafi nukililyarta.

A watan Mayun shekarar 2018, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da janye jiki daga yarjejeniyar da Iran ta rattaba hannu tare da bangarorin da abin ya shafa a shekarar 2015 dangane da batun nukiliyarta. Daga baya kuma gwamnatin Amurka ta sake sanyawa Iran takunkumin da aka riga aka dakatar da shi sakamakon yarjejeniyar, wanda ya shafi fannonin man fetur, kudi, da sufuriin jiragen ruwa da dai sauransu, lamarin da ya matsawa Iran lamba sosai a fannonin zaman rayuwar jama'a da tattalin arzikinta.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China