190313-Bilkisu.m4a
|
Dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa za ta kasance sabuwar babbar dokar kasar Sin a fannin zuba jari na baki 'yan kasuwa, ana kuma fatan dokar za ta kyautata tare da kirkiro tsarin dokokin zuba jari na 'baki 'yan kasuwa na kasar. Wani muhimmin abu dake cikinta shi ne, ta yi tanadi wani sabon tsari, wato masu zuba jari na kasashen ketare za su samu dama iri daya da takwarorinsu na kasar Sin a yayin da suke neman zuba jari a kasuwar kasar, baya ga haka, ban da sassan da baki 'yan kasuwa da a baya ba za su iya zuba jari ba, baki 'yan kasuwa za su samu matsayin daya da takwarorinsu na kasar Sin wajen zuba jari a kasar.
Dan majalisar CPPCC, kuma babban masani a fannin tattalin arziki na sashen nazarin takardun lamunin kudi na Shenwan Hongyuan, Yang Chengzhang yana ganin cewa, an tanadi wasu abubuwa da dama a cikin daftarin ne sakamakon fasahohin da aka samu wajen tsarin gudanar da harkokin sassan da baki ba za su zuba jari ba a yankunan cinikayya cikin 'yanci.
"Tun a shekarar 2013 muka soma kafa yankin cinikayya cikin 'yanci na Shanghai, wani muhimmin aikin da aka yi wajen gudanar da harkokin yankin, shi ne dakatar da dokokin jarin waje uku da ake amfani da su a da, wadanda suka hada da 'dokar kamfanonin hadin-gwiwar jarin gida da waje', da 'dokar kamfanonin jarin waje', gami da 'dokar kamfanonin da Sin da kasashen waje suka kafa tare', tare kuma da gudanar da harkoki bisa tsarin sassan da baki ba za su zuba jari ba. Ba kamar yadda muka saba yi a da ba, akwai bukatar mu tattara wasu fasahohi da dama wajen tafiyar da tsarin, yanzu muna amfani da hanyar da ta dace da dokokin kasa da kasa, kuma wadanda suka dace da zamani a duniya wajen kula da jarin waje."
'Yar majalisar CPPCC, kuma mataimakiyar shugaban kamfanin Deloitte madam Jiang Ying ta bayyana cewa, daftarin dokar zuba jari na baki 'yan kasuwa ta kawar da damuwar 'yan kasuwar kasashen waje, za kuma ta karfafa musu gwiwa wajen zuba jari a nan kasar Sin, a sa'i daya kuma, ta nuna inganta tafiyar da harkokin gwamnatin kasar Sin. Ta ce,
"Daftarin dokar mai adalci da tabbaci kuma a bayyane, ya karfafa imanin baki 'yan kasuwa wajen zuba jari a nan kasar Sin. Kamata ya yi gwamnati ta baiwa jarin waje 'yanci, da sa ido kansa sosai, tare kuma da ba su hidima a dukkan fannoni, ban da wannan kuma, ya kamata a bullo da wani tsarin na gabatar da korafi. Ana iya gano alamarta a cikin wannan daftarin dokar, kan yadda ayyukan gwamnatin kasa ke sauyawa."
Kafin haka, wasu mutane sun damu cewa, mai yiwuwa ne dokar jarin waje ta baki 'yan kasuwa za ta yi mummunan tasiri kan kamfanonin da ba na gwamnati ba na kasar Sin. Game da haka, 'yan majalisar CPPCC, masu masana'antun da ba na gwamnati ba, daraktan zartaswa na kamfanin kimiya na JiaDu mista Liu Wei ya bayyana cewa, baya ga yadda kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin dake maraba da baki 'yan kasuwa don su zuba jari a nan kasar Sin, za kuma su ci gajiya ddaga dokar, suna da imani da karfin tinkarar duk wasu kalubaloli da za su iya kunno kai. Ya ce,
"Yanzu a kasuwar kimiyya, kamfanonin kasar Sin da karfin nazari na kasar suna da karfin yin takara sosai, musamman ma yadda suka fahimci kasuwar kasar Sin sosai, don haka, ya kamata mu cimma ra'ayi daya kan wannan doka."
Game da wannan batu, mataimakin daraktan kwamitin tattalin arziki na CPPCC Liu Shijin ya bayyana cewa, daftarin ya tanadi yadda za a gudanar da dokokin bai daya a tsakanin kamfanoni na cikin gida da na waje, hakan zai taimaka wajen samar da wani yanayin kasuwa mai zaman karko da adalci da kuma bayanai a fili. A cewarsa,
"Bayan zartas da wannan doka, za ta taka muhimmiyar rawa wajen kwantar da hankalin kamfanoni masu jarin waje, ta yadda za su nemi ci gaba mai dorewa a nan kasar Sin. Ban da wannan kuma, za ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa tsarin tattalin arzikin kasuwanci na kasar Sin, da wani muhallin takara mai adalci." (Bilkisu)