190312-Masanan-Najeriya-sun-ce-kamata-ya-yi-kasarsu-ta-yi-amfani-da-shawarar-ziri-daya-da-hanya-daya-don-neman-bunkasuwa-Murtala.m4a
|
A karshen watan Afrilun bana, za'a yi taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasa da kasa ta fannin shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Game da wannan batu, darektan zartaswa na sashen nazarin harkokin Najeriya na cibiyar nazarin batutuwan Afirka dake jami'ar horas da malamai a lardin Zhejiang na kasar Sin, Dr. Ehizuelen Michael ya bayyana cewa, "ziri daya da hanya daya" ta kara mu'amala da cudanya tsakanin kasashe da yankuna daban-daban a fadin duniya, kana shawara ce dake samar da wani sabon salon hadin-gwiwar kasa da kasa mai kawo moriyar juna. Dr. Michael ya ce, hada kai tare da kasar Sin wajen aiwatar da "ziri daya da hanya daya" na da babbar ma'ana ga Najeriya wadda ke dogara kusan kacokan kan albarkatun mai. Dr. Michael ya ce:
"Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dade tana nuna kwazo wajen raya tattalin arzikin ta ta hanyoyi daban-daban, tana kuma kokarin horas da wasu mutane ta yadda za su kware a fannin bunkasa tattalin arziki ta sabbin hanyoyi. Idan Najeriya ta shiga shawarar 'ziri daya da hanya daya', hakan zai taimaka ga habaka hadin-gwiwa da kasar Sin da sauran kasashe ta fannin tattalin arziki da kasuwanci, da samar da damammakin bunkasuwa iri daban-daban ga kasar, al'amarin da zai taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyi daban-daban. A halin yanzu, ana fuskantar matsalar bada kariya ga harkokin kasuwanci, kuma duniya na kara fuskantar abubuwan rashin tabbas a fannin tattalin arzikin, amma duk da haka, dunkulewar duniya baki daya ita ce makoma mai kyau. A wannan halin da ake ciki, ina tsammanin shawarar 'ziri daya da hanya daya'da gwamnatin kasar Sin ta gabatar, za ta taka muhimmiyar rawa wajen hade kan kasashe gami da yankuna daban-daban a duniya."
Nahiyar Afirka muhimmiyar memba ce a cikin shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma bana ita ce shekarar farko da Najeriya ta fara aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya." A nasa bangaren, Dr. Sheriff Ghali Ibrahim, malami dake koyarwa a fannin kimiyyar siyasa da alaka ta kasa da kasa a jami'ar Abuja yana ganin cewa, duba da irin nasarorin da aka samu a wasu kasashen Afirka wajen aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", Najeriya, a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki kana mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka, ya kamata ta yi amfani da wannan dama. Dr. Sheriff ya bayyana cewa, yana fatan a cikin wa'adin mulkinsa na biyu, shugaba Muhammadu Buhari zai kara nazartar halin da kasarsa ke ciki, da kara hada kai tare da gwamnatin kasar Sin wajen aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya', inda ya ce:
"An riga an samu sakamako mai kyau wajen aiwatar da 'ziri daya da hanya daya' a kasashen Kenya da Djibouti da Masar da wasu kasashen Afirka. Haka kuma shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce ko da yaushe kofar kasar Sin a bude take ga duk kasar dake son shiga shawarar 'ziri daya da hanya daya'. A halin yanzu Najeriya ma ta kammala wasu ayyukan da suka shafi wannan shawara, ciki har da jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna. Muna fatan gwamnatin Buhari za ta ci gaba da kokari wajen inganta hadin-gwiwa tare da kasar Sin a wannan fanni."(Murtala Zhang)