in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin raya yankunan Guangdong-HK-Macau na kasar Sin
2019-03-11 20:32:23 cri

Tun bayan da gwamnatin kasar Sin ta fitar da shirin raya yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau a watan Fabrairun bana, an lura cewa, rahotannin da kafofin watsa labaran kasashen duniya suke bayarwa kan batun, wadanda yawansu ya kai kaso 98.7 bisa dari, na nuna yabo kan matakan da gwamnatin kasar Sin take dauka.

Yanzu haka a yayin da ake gudanar da taruka biyu wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da taron majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasa, batutuwa game da yadda za a gina yankunan, da kuma yadda za a bunkasa yankunan, su ne suka fi jawo hankalin wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar, da mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, wadanda suka zo daga lardin Guangdong, da yankunan musamman na kasar wato Hong Kong da kuma Macau.

Idan aka kwatanta yankunan da sauran shahararrun yankuna masu ci gaba a fadin duniya, kamar su yankin tafiyar da harkar kudi na New York, da yankin kimiyya da fasaha na San Francisco na kasar Amurka, da yankin masana'antu na Tokyo a kasar Japan, yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau na iya zama a matsayin sabbin yankunan da gwamnatin kasar Sin take dukufa wajen raya tattalin arzikin su ba tare da rufa rufa ba.

Ana iya cewa, ba a taba ganin irin wannan salon raya tattalin arziki a tarihi ba a fadin duniya, inda ake gudanar da harkokin kasa a cikin kasa guda bisa tsarin zamantakewar al'umma iri biyu, kuma aka kafa yankunan kwastam guda uku, tare kuma da yin amfani da kudi iri uku, da kuma tsarin doka iri uku, kuma domin cimma burin raya tattalin arziki mai inganci a yankunan dole ne a tsara wani tsari na kirkire-kirkire.

Bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, a cikin shekarar bana da ake ciki, za a mai da hankali kan aikin tsara manufofin dake da nasaba da hakan, ta yadda za a samar da karin damammaki ga matasan Hong Kong-Macau domin su kafa kamfanoni a lardin Guangdong.

Hakika, a cikin shekaru 40 da suka gabata, wato tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyaran fuska a gida, da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, ana gudanar da hadin gwiwa tsakanin yankunan nan uku, wato lardin Guangdong da yankin Hong Kong da kuma yankin Macau yadda ya kamata, musamman ma tun bayan da gwamnatin kasar Sin ta maido da mulkinta a yankunan Hong Kong da Macau, inda hadin gwiwar dake tsakaninsu ya kara zurfafa sannu a hankali. Misali a shekarar 2003, babban yankin kasar Sin ya kulla yarjejeniyar CEPA tsakaninsa da yankin Hong Kong da Macau, domin kara karfafa huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, tare kuma da kara karfafa alakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya.

Ko shakka babu tattalin arzikin yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau ya samu ci gaba cikin sauri, wato fadin yankunan ya kai daukacin fadin yankuna uku na New York da San Francisco da kuma Tokyo, kana adadin manyan akwatunan zuba kayayyakin da ake jigilar su a tasoshin yankunan ya ninka na daukacin sauran yankunan uku har sau 4.5, amma idan ana son ingiza ci gaban yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau bisa ma'aunin koli a fadin duniya, ya zama wajibi a kara mai da hankali kan kirkire-kirkire a fannin tsara manufofi, bisa tushen koyon fasahohin zamanin da suka kai sahun gaba a fadin duniya.

Masanan da abin ya shafa sun yi nuni da cewa, ana sa ran kirkire-kirkire wajen harkar kudi, za su taka muhimmiyar rawa yayin da ake kokarin raya yankunan, dalilin da ya sa haka shi ne, domin yankin musamman na Hong Kong babbar cibiya ce ta harkar kudi a fadin duniya, kuma idan an gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin lardin Guangdong da yankin Hong Kong da yankin Macau, hakan zai iyar samar da isasshen kudin da ake bukata wajen kyautata sana'ar kere-kere, da kuma kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha.

Har kullum Sinawa dake zaune a lardin Guangdong, da yankin Hong Kong, da kuma yankin Macau, suna kwazo da himma kan aikinsu. An ce ana gudanar da ayyukan gwaji guda 40 a lardin Guangdong, domin kara kyautata muhallin kasuwanci da hidimar kirkire-kirkiren harkar kudi. A bayyane take cewa, ci gaban yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau, zai kasance abin koyi ga sauran kasashe. Domin cimma wannan buri, gwamnatin kasar Sin za ta kara sanya kokari matuka daga duk fannoni.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China