in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Wengang: Ya kamata a kara yin mu'amala tsakanin Sin da Najeriya a fanonnin da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum
2019-03-11 13:44:23 cri

A kwanan baya, Mr. Li Wengang, wani masani dake nazarin batutuwan Najeriya a sashen nazarin batutuwan Afirka na cibiyar nazarin harkokin zaman al'umma ta kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, ya kamata kasashen Sin da Najeriya su mai da hankulansu wajen kara yin mu'amala a fannonin da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum a lokacin da suke aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya".

A yayin taron manema labaru da aka shirya a ran 8 ga wata, Mr. Wang Yi, mamban majalisar gudanarwa kana ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, za a yi taron kolin tattaunawar hadin gwiwa karo na biyu kan shawarar "ziri daya da hanya daya" a nan Beijing a karshen watan Afrilu. Wannan shi ne aikin diflomasiyya mafi muhimmanci da kasar Sin za ta shirya a gida a bana, tabbas zai jawo hankulan kasashen duniya baki daya.

Li Wengang ya bayyana cewa, kasar Najeriya, kasa mafi yawan mutane a nahiyar Afirka, kana kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka. A 'yan shekarun baya, kasashen Sin da Najeriya sun yi hadin gwiwa har ma sun samu kyawawan sakamako a fannin samar da kayayyakin more rayuwar jama'a, alal misali, shimfida layukan dogo, da hanyoyin mota, da zauren jiran fasinjoji na filin saukar jiragen sama, da tasoshin teku da yankunan raya masana'antu da na cinikayya maras shinge ba da makamatansu. Sannan kayayyaki "Kirar Najeriya" da 'yan kasuwan Najeriya suka samar bisa hadin gwiwar da suke yi da takwarorinsu na Sin na samun karbuwa a kasuwar Najeriya. A cikin shekaru 4 da suka gabata, shugaban Najeriya mai ci Muhammadu Buhari ya kawo ziyara kasar Sin har sau biyu, ya kuma gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping a wasu tarukan kasa da kasa, inda ya bayyana fatansa na karfafa yin hadin gwiwa da mu'amala da kasar Sin. A watan Satumban shekarar 2018, a yayin taron kolin FOCAC da aka shirya a nan Beijing, gwamnatocin Sin da Najeriya sun sa hannu kan wata takardar hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya". Sakamakon haka, shekarar 2019 ta zama shekara ta farko da kasar Najeriya ta zama mamban shirin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya".

A ganin Li Wengang, ba ma kawai shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta amfanawa bunkasar tattalin arzikin Najeriya ba, har ma za ta amfanawa mu'amalar fannonin dake shafar bil Adama na yau da kullum tsakanin kasashen biyu. Mr. Li Wengang yana mai cewa, "Bunkasa tattalin arziki ya zama aiki mafi muhimmanci a wa'adi na biyu na shugaba Buhari. A ganina, aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya' a Najeriya zai taimakawa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Najeriya a fannoni daban daban. A bangare daya kuma, a cikin rahoton aikin gwamnati na bana, an nuna cewa, za a karfafa mu'amalar abubuwan dake shafar bil Adama na yau da kullum tsakanin Sin da kasashen waje, domin inganta rayuwar jama'a. Najeriya kasa ce mai arzikin al'adun gargajiya, Nollywood din Najeriya ya yi suna sosai wajen samar da fina-finai. Sabo da haka, ina tsammanin ya kamata kasashen Sin da Najeriya su kara yin hadin gwiwa a fannin tsara fina-finai. Yanzu, wasu fina-finai da wasannin kwaikwayon talibijin na kasar Sin da aka fassara su daga Sinanci zuwa harshen Hausa, na samun karbuwa a kasar Najeriya. Sakamakon haka, a ganina, kara yin mu'amala a fannonin dake shafar bil adama na yau da kullum yana da muhimmanci sosai ga kokarin tabbatar da ganin shawarar 'ziri daya da hanya daya' ta zauna a kasar Najeriya."

A yayin taron kolin FOCAC da aka shirya a nan Beijing a bara, shugaba Xi Jinping ya bayyana fatansa na yin hadin gwiwa tare da Afirka wajen kafa al'umma mai makoma daya ga dukkanin bil Adama bisa mu'amala da bunkasar al'adunsu, ta yadda abubuwan dake shafar bil Adam na yau da kullum na Sin da Afirka za su yi koyi da yin mu'amala da juna, da kuma kasancewa tare. Lamarin ya sa Li Wengang ya bayyana cewa, kara yin mu'amalar al'adu yana da muhimmanci sosai ga kokarin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" tsakanin Sin da Najeriya, har ma tsakanin Sin da Afirka.

"A hakika dai, bambancin al'adu shi ne dalilin da ya sa aka gamu da dimbin matsaloli na rashin fahimtar juna tsakanin Sin da Afirka. A ganina, kasashen Sin da Afirka suna bukatar kara fahimtar juna domin cimma moriya daya. Bai kamata a manta da mabanbantan mu'amala da kuma musayar ra'ayoyinsu kan al'adu da wayin kai a lokacin da ake aiwatar da shawawar 'ziri daya da hanya daya' ba. Yanzu daliban Afirka da yawa suna karatu a nan kasar Sin, wasu daliban Sinawa ma suna koyon harsunan Afirka a sassan daban-daban na Afirka, irin wannan kokari zai amfanawa al'ummomin Sinawa da na Afirka su kara fahimtar juna. Bugu da kari, cibiyar nazarin Afirka da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shelanta kafuwa za a bude ta ne a watan Afrilun bana. Tabbas wannan cibiya, za ta taka muhimmiyar rawa ga cudanyar fannonin dake shafar rayuwar bil Adama na yau da kullum tsakanin Sin da Afirka." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China