in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na makokin babbar jami'arta da ta mutu a hatsarin jirgin saman Ethiopia
2019-03-12 09:52:31 cri

Wakilin musammam na shugaban hukumar AU a Somalia, Francisco Madeira, na jimamin mutuwar babbar jami'ar shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar a hatsarin jirgin saman Ethiopia.

Francisco Madeira, ya ce ya kadu da jin mutuwar Christine Alalo, wadda ta kasance mukaddashiyar kwamishinan 'yan sanda a shirin AMISOM na AU mai wanzar da zaman lafiya a Somalia.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a Mogadishu, jami'in ya ce Christine Alalo 'yar asalin kasar Uganda na daga cikin mutane 157 da suka mutu a hatsarin jirgin saman Ethiopia mai lamba 302, bayan ya tashi da minti 6 daga birnin Addis Ababa, domin zuwa Nairobin Kenya a ranar Lahadi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China