in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen Habasha ya ce an gano na'urorin nadar bayanai daga jirgin sa da ya yi hadari
2019-03-11 20:33:01 cri

Kamfanin jiragen sama na kasar Habasha wato Ethiopian Airline, ya ce an gano na'urorin nadar rubutattun bayanai da masu sauti, daga cikin jirgin sa da ya yi hadari.

Wata sanarwa da mahukuntan kamfanin suka fitar ta bayyana hakan a yau Litinin, tana mai cewa sakamakon ci gaba da binciken da ake yi game da hadarin jirgin saman kamfanin da ya auku a jiya Lahadi, an yi nasarar gano na'urorin nadar bayanan sa, ko da yake dai hadarin ya sabbasa rasuwar daukacin mutane 157 dake cikin jirgin.

Kaza lika sanarwar ta ce, kamfanin na Ethiopian airline na ci gaba da lura da wannan al'amari tare da sauran masu ruwa da tsaki, yana kuma bayar da dukkanin hadin kai da tallafi, ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da rayukan su, a wata cibiyar wucin gadi dake birnin Addis Ababa, da kuma filin saukar jirage dake birnin Nairobin kasar Kenya.

Kafin hakan, kamfanin na Ethiopian Airlines ya bayyana aniyar sa, ta dakatar da amfani da samfurin jirgin sama kirar 737-Max 8, wanda irin sa ne ya yi hadari da safiyar jiya Lahadi.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China