in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dukkan mutane 157 a jirgin saman Habasha sun mutu bayan da jirgin ya yi hadari
2019-03-10 20:12:08 cri

Gidan talabijin din kasar Habasha ya rawaito cewa, dukkan mutane 157 dake cikin jirgin saman Ethiopian Airlines (ET), an tabbatar da mutuwarsu bayan da jirgin ya yi hadari a safiyar yau Lahadi.

Dukkan fasinjoji 149 da ma'aikatan jirgin su 8 na kamfanin ET 302 sun hallaka, yayin da jirgin ke kan hanyarsa zuwa birnin Nairobi, kasar Kenya, kamar gidan talabijin na kasar (EBC) ya ba da rahoton.

Jirgin saman samfurin Boeing 737-800 MAX, ya tashi ne da misalin karfe 08:38 na safe agogon kasar daga filin jirgin saman kasa da kasa na Bole dake Addis Ababa, jirgin ya fuskanci matsalar katsewar hanyoyin sadarwa ne da misalin karfe 08:44 na safe, in ji kamfanin jirgin saman.

A wata sanarwa daga ofishin firaiministan kasar Habashan, ya bayyana damuwa tare da jajantawa iyalan da masoyan wadanda hadarin ya rutsa da su.

Jirgin dai ya yi hadarin ne a kusa da birnin Bishoftu, mai tazarar kilomita 45 daga kudu maso gabashin Addis Ababa, in ji sanarwar kamfanin jirgin na ET.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China