Lu kang wanda ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya da dare, ya kuma yi amfani da wannan dama wajen mika sakon ta'aziya da iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu a sakamakon wannan hadari.
Ya ce, kasar Sin tana fatan bangaren Habasha, zai yi kokarin gano musabbabin faruwar hadarin jirgin ba tare da bata lokaci ba, kana ya sanar da bangaren kasar Sin sakamakon bincken.
Jirgin saman kamfanin jiragen saman na kasar Habasha kirar Boeing 737-800 MAX, yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Nairobin kasar Kenya, a lokacin da ya fadi jim kadan da tashin sa jiya daga Addis Ababan,babban birnin kasar Habasha jiya Lahadi da safe agogon wurin, inda ya halaka dukkan fasinjoji 157 da kuma ma'aikatan jirgin 8 .(Ibrahim)