in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar ISA ta bukaci nahiyar Afrika ta samar da makamshi daga hasken rana
2019-03-11 13:06:44 cri

Kungiyar kasashe masu sarrafa hasken rana domin samun makashi ISA, Ta bukaci kasashen nahiyar Afrika da su rika samar da makamashi daga hasken rana domin kare muhallansu.

Jakadiyar shirin kungiyar ISA, Mohua Mukherjee, ta shaidawa wani taron manema labarai a Nairobin Kenya cewa, galibin kasashen Afrika sun kasance ne a wuraren dake da hasken rana, dake da dimbin albarkatun makamashi.

Mohua Mukherjee, ta bayyana yayin taro na 2 na MDD kan kimiyya da dabaru da kasuwanci da suka shafi muhalli cewa, ya kamata kasashen Afrika su ci gajiyar raguwar tsadar fasahar sarrafa hasken rana domin cimma burin samun makamashi mai tsafta da suke muradi.

Ta ce gidajen da yawa daga cikin mazauna nahiyar ba sa hade da turakun lantarki na kasashensu.

Ta kara da cewa, wannan ya samar da gagrumar dama ga 'yan Afrika da su yi amfani da fasahar sarrafa hasken rana domin amfani da kayakinsu na laturoni.

Jakadiyar ta ce kungiyar ISA za ta yi amfani da hadin gwiwarta da Afrika ta kudu, domin ba sauran kasashen nahiyar damar amafana, tare kuma da samun gogewa daga takwarorinsu na sauran kasashe masu tasowa ta yadda za su rungumi fasahar sarrafa hasken rana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China