Shugabar hukumar Vera Songwe, ta bayyana haka ne a jiya, yayin wani taron manyan jami'ai kan kiwon lafiya da ya gudana a Addis Ababa na Habasha, wanda hukumar lafiya ta duniya ta shirya. A cewarta, nahiyar Afrika ta samu gagarumar ci gaba a bangaren kiwon lafiya cikin wasu shekaru da suka gabata.
Ta ce tun daga 1990 zuwa 2015, tsawon rayuwar mutane ya karu daga shekaru 54 zuwa 63. Sannan, adadin matan da suke mutuwa yayin haihuwa da yaran da suke mutuwa kafin shekaru 5, ya ragu da kusan rabi a tsakanin wadancan shekaru.
Sai dai Vera Songwe ta kuma jadadda cewa, duk da ci gaban da aka samu a bangaren kiwon lafiya, ya kamata a kara karfafa kokari wajen cimma mizanin ingantuwar kiwon lafiya na nahiyar da duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)