in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude cibiyar nazarin bayanai dangane da Sin da Afrika a Johannesburg
2018-11-23 11:20:22 cri
An bude cibiyar nazarin bayanai dangane da Kasar Sin da Afrika, a jami'ar Johannesburg na Afrika ta kudu a jiya Alhamis.

Ana sa ran cibiyar ta CACS mai jami'ai da malamai, ta taka muhimmiyar rawa wajen tattara bayanai da bitar ci gaban dangantakar Sin da Afrika.

A cewar David Monyae, Daraktan cibiyar, kuma daya daga cikin daraktocin kwalejin Confucius dake Jami'ar ta Johannesburg, ana samun bayanai na karya game da dangantakar Sin da Afrika ne saboda rashin sahihan bayanai ga al'umma.

Ya ce cibiyar za ta mayar da hankali kan dangantakar Sin da Afrika, da kuma auna tasirin manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa a Afrika, ciki har da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da zamanantar da ayyukan masana'antu da musaya tsakanin jama'ar bangarorin biyu da kuma alakar bangarorin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China