in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon daidaita takunkumai kan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
2019-02-22 10:15:45 cri
Zaunannen wakilin Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya ce kasar Sin na goyon bayan kwamitin sulhu na MDD, wajen daidaita wasu takunkuman da aka sanyawa Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, bisa sauyawar yanayin kasar.

Ma Zhaoxu, ya bayyanawa taron kwamitin sulhun kan Jamhuriyar Afrika ta tsakiya cewa, yayin da yanayi a kasar ke gyaruwa, kasar Sin na goyon bayan kwamitin, ya duba yanayin da ake ciki da kuma buri da bukatun kasar, wajen daidaita wasu takunkumai.

Ya kara da cewa, manufar sanyawa kasar takunkumi ita ce, mayar da ita kan turbar zaman lafiya, da kiyaye doka da oda, yana mai cewa muhimmin abu a yanzu shi ne, taimaka mata wajen samun sulhu da zaman lafiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China