in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta bunkasa bangaren albarkatun ruwanta ba tare da gurbata muhalli ba
2019-03-11 11:33:41 cri

Ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin, ta bayyana cewa, kasar za ta bunkasa bangaren albarkatun ruwanta ba tare da gurbata muhalli ba. Tana kuma yi fatan sama da kaso 98 cikin 100 na albarkatun ruwa da za ta samar, za su kai ingancin da kasuwa ke bukata nan da shekarar 2022, yayin da ake fatan yankunan muhallin halittu na gwaji kuma, za su kai kaso 65 cikin 100 na yankunan da ake noman albarkatun ruwa.

A kokarin da ake na ganin an cimma wannan nasara,sassan gwamnati da suka hada da ma'aikatar aikin gonan kasar, sun fito da wasu dokoki game da yadda za a raya sashen ba tare da gurbata muhallai ba, inda ake fatan gina karin shiyoyin gwaji da matakan kare cututtukan dake shafar muhallin albarkatun ruwa.

A bisa tsarin,a yayin da ake kara tsara hanyoyin ruwa da wurare masu zurfi da ambarkatun ruwan za su rika amfani da shi, a hannu guda kuma kasar Sin, za ta yi kokarin inganta sashen da ma karfafa gwiwar kiwon albarkatun ruwa a wurare masu zurfi.

Bugu da kari, dokar ta kara jaddada cewa, mahukuntan kasar Sin,za su inganta yadda za a sarrafa dagwalon da ake fitarwa da kara karfafa rawar da sashen ke taka wajen kare muhallin halittu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China