Rahotan wadda cibiyar watsa labaran Intanet ta kasar Sin ta fitar, ya nuna cewa, an samu bunkasuwar wannan sashe a kasar Sin, kuma ya zuwa watan Oktoban shekarar 2018, an baiwa sama da kamfanoni 100 iznin tafiyar da hidimar motocin haya ta intanet a wasu biranen kasar.
Rahotan ya kara da cewa, wannam bangaren yana samun karuwar motoci masu amfani da sabbin makamashi da ke amfani da wutar lantarki kai tsaye ko kalilan, inda ake fatan daina amfani da motocin dake amfani da tsoffin makamashi.
Bugu da kari, ana kara daukar matakan inganta dokokin tafiyar da hidimar motocin haya ta intanet da kare lafiya da muradun fasinjoji.(Ibrahim)