Kalaman jami'in na AU na zuwa ne bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta sanar da sakamakon wucin gadi na zaben shugabancin kasar.
An ruwaito Moussa cikin wata sanarwa na cewa, kamata ya yi a kalubalanci sakamakon zaben na wucin gadi bisa doron doka cikin lumana, da ma tattaunawar siyasa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki na kasar.
Sai dai kuma Faki, ya ce yanayin da ake ciki a kasar na bukatar cimma daidaito, ta hanyar mutunta manufofin demokiradiya da 'yancin dan-Adam da ma kokarin tabbatar da zaman lafiya.
A jiya da safe ne, hukumar zaben kasar ta ayyana dan takarar adawa Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar, sai dai kuma ragowar 'yan takarar sun ti watsi da sakamakon zaben. (Ibrahim)