in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin CMG ya kulla yarjejeniyar zurfafa hadin gwiwa da gwamnatin lardin Guangdong na kasar Sin
2019-03-02 20:21:14 cri

A yau Asabar, babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG da gwamnatin ladin Guangdong dake kudancin kasar, suka kulla yarjejeniyar zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Bisa yarjejeniyar da aka kulla, kamfanin CMG zai kafa reshensa na yankin Guangdong-Hongkong-Macao da kuma na lardin Guangdong a birnin Guangzhou, sa'an nan zai kafa cibiyar tsara labaru a birnin Shenzhen. Haka zalika, kamfanin CMG da gwamnatin lardin Guangdong za su kafa wani tsari na hadin gwiwa a fannin tsara fina-finai da shirye-shiryen telabijin, gami da zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin fasahohin 5G, da na samar da hotunan bidiyo mai inganci sosai na 4K da dai sauransu.
Sabbin rassan da kamfanin CMG zai kafa a lardin Guangdong sun biyo bayan rassansa na birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, wadanda ya fara ginawa a watan Oktoban bara.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China