Yi Gang ya bayyana hakan a gun taron manema labaru na taro na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a wannan rana.
Yi Gang ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun tattauna kan yadda za a girmama ikon tsaida manufofin kudi da juna, da bin ka'idar tsaida tsarin farashin musayar kudi bisa kasuwa, da ya kamata bangarorin biyu su cika alkawarinsu da aka gabatar a gun taron koli na kungiyar G20, kamar su kada a rage darajar kudi domin yin takara, da gujewa yin amfani da tsarin farashin musayar kudi domin yin takara, da kara yin mu'amala sosai a kasuwar musayar kudi, da kuma yin alkawarin gabatar da alkalumansu bisa ma'aunin asusun bada lamuni na duniya wato IMF. (Zainab)