'Dan jarida Ongango Victor ya bayyana cewa, bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", da tsarin dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka, kasashen Kenya da Sin na karfafa cudanya da hadin kai ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. Ya bada Misalin cewa, cimma nasarar gina hanyar dogo ta Mombasa-Nairobi ya sa kaimi ga saurin ci gaban kasar Kenya a fannonin sufuri da jigilar kayayyaki da kuma cinikayya. A daya bangaren kuma, ya samar da guraban aikin yi sama da dubu 50 a wurin.
A nasa bangaren, Deo Kamagi daga jaridar Daily News ta kasar Tanzaniya shi ma ya nuna cewa, ci gaban kasashen Afirka na bukatar goyon bayan kasar Sin a fannonin kudi da fasaha da kuma hazaka. Ya ce tsarin dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka da shawarar "Ziri daya da hanya daya" sun samar da dama da manufar samun ci gaba ga kasashen Afirka a lokacin da ya dace. (Bilkisu)