A yayin da yake bayani kan daftarin, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wang Chen ya bayyana cewa, tsara dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa muhimmin mataki ne da aka dauka don tabbatar da manufofin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na kara habaka bude kofa ga kasashen ketare, da ba baki damar zuba jari. Har ila yau, ya ce ta dace da yanayin da ake ciki, da inganta ci gaban dokar zuba jari ga baki, kuma ita ake bukata wajen raya tattalin arziki bisa tsarin gurguzu da kuma samun tattalin arziki mai matukar inganci.
Bisa daftarin, masu zuba jari na kasashen ketare za su samu dama iri daya da takwarorinsu na kasar Sin a yayin da suke neman zuba jari a kasuwar kasar, baya ga haka, ban da sassan da baki 'yan kasuwa ba za su iya zuba jari ba, baki 'yan kasuwa za su samu matsayin bai daya da takwarorinsu na kasar Sin wajen zuba jari a kasar. Ya kara da cewa, Kamfanonin waje dake zuba jari a kasar Sin na samun moriya daga manufofi daban daban da kasar Sin ta tsara na goyon bayan ci gabansu. (Bilkisu)