in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren soja na kasar Nijer ya harbe dakarun kungiyar Boko Haram 38 har lahira
2019-03-10 16:48:53 cri
Ma'aikatar tsaron kasar Nijer ta sanar a ranar 9 ga wata cewa, sojojin gwamnatin kasar sun harbe dakarun kungiyar Boko Haram 38 a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar a kwanakin baya.

A wata sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar Nijer ta bayar, an ce, dakarun kungiyar Boko Haram sun kai hari ga wani sansanin soja dake jihar Diffa a daren ranar 8 ga wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane 7 tare da raunatar mutane fiye da 20. Bangaren soja na kasar Nijer ya mayar da martani nan take, inda suka harbe dakarun kungiyar Boko Haram 38, da lalata motoci 5, sannan ta kama wani dan kungiyar, da kuma samun makamai da dama.

Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin kasar Nijer za su dauki matakai a wannan yanki don murkushe sauran dakarun kungiyar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China