in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari ga wani sansanin soja dake kudu maso gabashin kasar Nijer
2019-02-17 16:38:46 cri
Dakarun kungiyar Boko Haran sun kai hari kan wani sansanin soja na jihar Diffa dake kudu maso gabashin Jamhuriyyar Nijer a ranar 15 ga wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane 8.

Hukumar tsaron kasar Nijer ta gabatar da sanarwa a ranar 16 ga wata cewa, dakarun kungiyar Boko Haram sun kai hari ga wani sansanin soja na jihar Diffa dake kudu maso gabashin Jamhuriyyar Nijer a daren ranar 15 ga wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane 8 tare da raunatar mutane 29. Bangaren soja na Jamhuriyyar Nijer ya mayar da martani tun da wuri, ya zuwa yanzu an kama dakaru 4 tare da motoci 4.

Jihar Diffa tana kan iyakar tsakanin Nijer da Nijeriya, kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-haren ta'addanci a wannan yanki, wadanda suka haddasa mutuwa da raunatar mutane da dama. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China