Gwamnatin kasar Kamaru ta ce, za ta yi kokarin inganta fasaha da damarmaki ga mata a sana'ar fasahar zamani, a wani bangaren na matakan jan hankalin karin 'yan mata zuwa fannin.
Ministan sadarwa na kasar Minette Libom Li Likeng, ya ce samun karin mata a sana'ar zai kara samar musu da 'yanci da karfafa ci gabansu.
Ya ce tattalin arziki fasahar zamani shi ne makomar kasarsu da nahiyar Afrika, domin yana taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin kasashe masu tasowa, yana mai cewa, za su lalubo ingantattun hanyoyin karfafawa gwiwar mata dake sana'ar. (Fa'iza Mustapha)