in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An raunata sojoji 12 bayan da 'yan bindiga suka bude wuta kan ayarin gwamna a Kamaru
2019-02-13 11:03:16 cri

Kimanin sojoji 12 da wani dan jarida guda aka jikkata a jiya Talata a lokacin da 'yan bindiga suka bude wuta kan wata tawagar gwamnan lardin Southwest, daya daga cikin yankuna biyu masu fama da rikici dake magana da yaren turanci a jamhuriyar Kamaru, kamar yadda hukumomin yankin suka tabbatar da hakan.

A cikin wata sanarwar, rundunar sojojin kasar ta ce, "a yayin da yake kai ziyara zuwa Kumba, tawagar gwamna Okalia Bilai ta sha ruwan alburusai a harin da mayakan 'yan awaren Ambazoniya suka kaddamar kan tagawar gwamnan. Sojoji uku sun samu munanan raunuka."

Hukumomin yankin sun fada cewa, an kaddamar da hari kan tawagar gwamnan ne a lokacin da yake kan hanyarsa zuwa ta'aziyya ga iyalan mutanen da suka rasa 'yan uwansu a sanadiyyar tashin gobara a wani asibiti wanda ya yi sanadiyyar hallaka mutane 4 a ranar Litinin.

Wani jami'in soja wanda ya nemi a sakaye sunansa fada wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, cewar gwamnan bai samu koda kwarzane ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China