Rev. Oliver Shey, babban jam'in gudanarwa na Kwalejin St. Augustine, ya ce 'yan bindigar sun je makarantar domin mika musu yaran, amma bayan sun lura da suka yi da kasancewar jami'an tsaro a makarantar, sai suka gaggauta dauke yaran tare da tafiya da su maboyarsu.
Kwalejin St Augustine, makarantar sakandare ce ta darikar Katolika dake garin Kumbo na yankin arewa maso yammacin Kamaru, daya daga cikin yankunan kasar 2, dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi, wadanda ke fama da rikici.
Rev. Oliver Shey ya ce sun bukaci sojojin su bar harabar makarantar domin ba 'yan bindigar damar dawo da daliban.
Ya ce maimakon dalibai 145 da suka sace ranar Asabar, 'yan bindigar sun shaida musu cewa yanzu suna tare da dalibai 200 kuma 170 daga cikinsu, daliban makarantar ne.
Har ila yau, ya ce dukka daliban da aka sace 'yan mata ne, sai kuma shugaban makarantar da masu gadi biyu da wani malami da iyalansa. (Fa'iza Mustapha)