Ministan kula da ilimi a matakin farko na kasar, Laurent Serge Etoundi Ngoa ne ya bayyana haka jiya a birnin Yaounde, yayin bikin ranar Harshen Uwa ta duniya.
Ya ce yanzu matakin ya zama tsari a hukumance, domin kasar ta na son a fara amfani da harsunan a dukkan makarantu.
Kamaru na da harsunan kabilu 260, amma Faransanci da da Ingilishi ne kadai harsunan da take amfani da su a hukumance.
Ministan ya ce manufar sabon matakin ita ce, mayar da harsunan kasar matsayin wadanda da za a rika amfani da su a hukumance a hankali. (Fa'iza Mustapha)