in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a tsaurara tsaro a Kamaru gabanin babban zaben kasar
2019-02-15 09:59:05 cri
Ministan kula da shiyyoyin Kamaru, Paul Atanga Nji, ya ce za a tsaurara matakan tsaro a shiyyoyi 10 na kasar kafin lokacin babban zabe.

Paul Atanga Nji, ya ce tsaro da zaman lafiya za su kasance manyan kalubalen da za su tunkara a 2019, musamman la'akari da zabuka da dama da za a shirya a bana, wadanda ya ce suna da muhimmanci ga demokuradiyyar kasar.

Ministan wanda ya bayyana haka a birnin Yaounde, lokacin da za a fara taron gwamnonin shiyyoyi, wanda ake yi sau 2 a shekara, ya ce ya kamata a dauki dukkan matakan da suka kamata, domin tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a dukkan cibiyoyi mulki.

Ana sa ran gudanar da zabukan 'yan majalisun dokoki da kananan hukumomi da na shiyyoyi a watan Satumba, yayin da ake tsaka da fama da karuwar barazana daga 'yan aware masu dauke da makamai a yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar, wadanda ke da rinjayen masu amfani da Turancin Ingilishi da kuma hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin arewa mai nisa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China