in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an MDD sun yi kira da a shigar da shugabanni mata cikin harkokin yanke shawara
2019-03-08 10:02:30 cri

Gabanin ranar mata ta duniya, da yawa daga cikin jami'an MDD, sun yi kira da a kara damawa da mata cikin harkokin da suka shafi yanke shawara da daukar matakai.

Shugabar babban taron majalisar Maria Fernanda Espinosa, ta bukaci kowa da kowa, su rubanya kokarinsu wajen kin jinin wariyar jinsi da cin zarafi mata da 'yan mata a kullum, tana mai cewa, akwai bukatar mata su ci gaba da shiga harkokin da suka shafi rayuwar al'umma da yanke shawara.

A nata bangaren, mataimakiyar Sakatare Janar na MDD Amina J. Mohammed, cewa ta yi, ba wa mata dama daidai da takwarorinsu maza a a fannin ayyukan yi, zai bude dimbin hanyoyi samun ci gaba. Haka kuma, ba za a iya cimma muradun ci gaba masu dorewa ba, matukar ba a damawa da mata yadda ya kamata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China