in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD: Akwai yiwuwar samun barkewar yaki tsakanin Falasdinu da Isra'ila
2019-02-22 10:34:25 cri

Nickolay Mladenov, jami'in MDD mai kula da aikin shimfida zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, ya furta a ranar Laraba cewa, bisa binciken da aka yi kan yanayin da ake ciki game da batun huldar dake tsakanin Falasdinu da Isra'ila, ana ganin cewa, da wuya a samu masalaha tsakanin bangarorin 2. Bisa la'akarin da samun karin rikici cikin wasu yankunan Falasdinu da kasar Isra'ila ta mamaye, yanzu ana fuskantar yiwuwar samun barkewar yaki tsakanin bangarorin 2.

Jami'in ya nanata cewa, don neman samun sulhu, ya wajaba a dauki wasu mataikai, wadanda suka hada da dakatar da habaka matsugunan Yahudawa, da baiwa Falasdinawa damar gudanar da harkokinsu a gabar yamma da kogin Jordan, da dai makamantansu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China