in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Antonio Guterres ya bukaci kasa da kasa su kawo karshen binne nakiyoyin karkashin kasa
2019-03-01 11:14:56 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya bukaci kasashen duniya da su kara kaimi wajen yaki da binne nakiyoyin karkashin kasa dake kashe jama'a.

Wata sanarwar wanda Stephane Dujarric, kakakin mista Guterres ya fitar ta ce, babban sakataren MDD ya yi maraba da cika shekaru 20 da fara aiki da yarjejeniyar MDD ta haramta binne nakiyoyin karkashin kasa dake hallaka al'umma a ranar 1 ga watan Maris, matakin ya taimaka wajen ceto rayukan al'umma da ba za su lissafu ba, hana nakasa jama'a da jikkata su da tabbatar da baiwa al'umma damar ci gaba da rayuwa.

Babban sakataren ya yabawa kokarin kasa da kasa wajen raba duniya da makamai wadanda suke kashewa tare da jikkata jama'a, wanda makaman na yin matukar tasiri wajen gurgunta zaman lafiya da ci gaban al'ummar duniya".

Guterres ya kuma taya kasashen duniya 31 da suka ayyana kansu a matsayin kasashen inda babu nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa, kana ya buakci dukkan kasashen duniya wadanda ba su kammala wannan shiri ba da su gaggauta yin hakan. Haka zalika ya bukaci kasashen duniya da su samar da kayayyakin tallafi ga dubban mutanen da nakiyoyi suka jikkata. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China