Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujjaric ya fitar, Antonio Guterres ya ce ya yi imani al'ummar kasar ba za su bari irin wannan tashin hankali ya dauke hankalinsu daga kokarinsu na samun zaman lafiya da kyakkyawar makoma ba.
Ya kuma jadadda goyon bayan MDD ga al'umma da gwamnatin kasar Somalia yayin da suke kokarin cimma zaman lafiya.
A kalla mutane 30 ne suka mutu sanadiyyar wani hari da aka kai cikin wata mota a wajen wani otel dake birnin Mogadishu, ranar Alhamis da dare.
Tuni dai kungiyar Al-Shabab mai alaka da Al-Qaeda ta dauki alhakin kai harin, tana mai cewa otel din ta kai wa hari, wanda ya yi fice tsakanin 'yan siyasa da jami'an gwamnati da kuma manyan 'yan kasuwa. (Fa'iza Mustapha)